Labarai
Mutane na cigaba da kokawa kan yadda farashin shinkafa ke kara ta’azzara a Nijeriya
Hauhauwar farashin Shinkafa dai na Kara ta’azara a Jihar Kano, dama wasu sassan kasar nan.
Sai dai mutane na hasashen cewa matsalar tsadar shinkafar ya samo asali ne tun lokacin da gwamnati ta umarni da a rufe iyakokin kasar nan, da hakan ya tilastawa mutane yin amfani da shinkafar ‘yar gida.
Sai dai kuma mutane na ganin kwalliya ba zata iya biyan kudin sabulu ba, duba da cewa, shinkafar da ake numawa a fadin kasar nan zata iya wadatar da su ne kadai in za’abi hanyoyin da ya kamata wajen sarrafa ta.
A binciken da Freedom Radio ta gano cewa, a lokuta da dama tsadar shinkafar kan kara habaka ne sakamakon su kansu manuman da suke dora buri akan shinkafar.
Yayin da wasu manoman suke alakanta hakan da tsadar taki, da kuma kayan inganta noman kansa.
Wasu masu sana’ar sayar da shinkafar da Freedom Radio ta zanta dasu sun ce a tun daga wajen da suke sarar shinkafar suke samunta da tsada, wanda hakan ke tilasta musu kara kudin.
Malam Muhammed Sani daya daga cikin masu sana’ar sodo wato Gyara Shinkafa daga samfera zuwa tsaba, wanda yace’ daga lokacin da ake dakko shinkafar daga gona, tun tana samfera zuwa gyaranta, da kawo ta kasuwa, dole tayi kudi, tunda kowanne aiki sai an iya kudinsa.
Burin talakan kasar nan dai bai wuce na ganin gwamnati ta saukaka musu hauhawar farashin kayan abincin ba a kullum, don shima ya rinka samu kamar sauran al’ummar kasar nan.
Rahoton: Nafi’u Abubakar Gafasa
You must be logged in to post a comment Login