Labarai
Farashin shinkafa ya karu tun bayan rufe boda
Kafin rufe iyakokin kasar nan da hukumar kwastam tayi farashin shinkafa na farawa ne daga naira dubu 17, na babban buhu mai cin kilo hamsin, a wasu lokutan ma wasu kan sayar da shi a naira dubu 14.
A yanzu kuwa farashin shinkafa yayi tashin gwauron zabi inda muddin mutum zai sami shinkafar waje farashin na farawa ne daga naira dubu 22 zuwa dubu 30.
yayin da ake sayar da shinkafa yar gida akan naira dubu 18 da dari biyar ko naira dubu 19 a wasu wuraren.
Duk kuwa da yadda al’umma suka koma noma ake kumar samar da shinkafa amma har kawo yanzu farashin bai sauka ba.
A kasuwar Garko dake jihar Kano ana fara sayar da shinkafa yar gida daga naira dubu 19 zuwa naira dubu 20.
Haka abin yake a wasu kasuwannin da suka hadar da na Kura da sauran sassan Kano.
A wasu garuruwan kuma kamar su Neja, da Benue, da Maitagari da ma jihar Jigawa duk farashin shinkafa na farawa ne daga naira dubu 18, dubu 19 wasu wuraren ma ta ta kaiwa har naira dubu 20.
Kamar yadda yadda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewar farashin kayayyaki ya karu da kimanin kaso 11 cikin dari tun daga watan Oktoban da ya gabata yayin da ya karu a wannan watan na Nuwamba da kimanin kusan kaso guda idan aka kwatanta da na baya.
Hukumar ta kara da cewa a watannin takwas da suka wuce a wannan shekara , an samu karuwar farashin kayyakin masarufi.