Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an tsaro sun matsa kaimi wajen ceto Fasinjojin da aka yi garkuwa da su a Edo

Published

on

Sojoji da ‘yan sanda da jami’an bijilanti a Jihar Edo sun zurfafa bincike don kuɓutar da mutanen da masu garkuwa da mutane suka sace.

Daga cikin wadanda akayi garkuwa dasu akwai Godwin Okpe da jami’an tsaro da wasu fasinjojin 29.
Sojoji da ‘yan sanda da jami’an vigilanti sun tsaurara bincike a tashar jirgin kasa da ke jihar Edo domin kuɓutar da fasinjoji 32 da aka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai mai kula da tashar, Godwin Okpe da shugaban jami’an tsaro, da aka bayyana sunansa da Ikhayere da fasinjoji 29.
‘Yan sanda dai sun ce suna iya kokarin su domin kuɓutar da fasinjoji’.

Wannan hari dai na zuwa ne watanni 10 bayan kazamin harin ‘yan bindiga kan jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna, wanda mutum 14 suka mutu tare da yin garkuwa da wasu 65.

Inda sai da aka shafe watanni da dama ‘yan bindigar sun saki fasinjojin bayan an biya kudin fansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!