Connect with us

Ƙetare

Farmakin dakarun RSF ya hallaka mutane 7 tare da raunata wasu 71 a Sudan

Published

on

Wani farmaki da Dakarun sa kai na RSF suka kai a yankin El-Fasher na kasar Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 tare da raunata wasu 71 a yankin, kamar yadda wata majiyar lafiya ta kasar ta sanar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ƙungiyar ‘yan RSF ta kaddamar da farmaki mafi muni a kan birnin da aka yi wa kawanya.

 

Rahotonni sun bayyana cewa, El-Fasher, babban birni na karshe a cikin babban yankin yammacin Darfur da har yanzu ke karkashin ikon sojoji, ya zama fagen daga mafi tashin hankali a yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun na RSF, wanda ya barke a watan Afrilun 2023.

 

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, dakarun sa-kai sun kara zafafa hare-haren da suka dade suna kai wa, suna dauke da manyan bindigogi da kuma kutsa kai cikin unguwannin da ke cike da jama’a, filin jirgin sama na birnin da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da ke fama da yunwa.

 

Rahotanni daga yankin na nuni cewa an sha kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitocin da ke ci gaba da aiki tare da kama hedikwatar ‘yan sandan yankin da RSF ta yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!