Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fashewar Gas: Mutane 9 ne suka mutu zuwa yanzu – SEMA

Published

on

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta ce zuwa yanzu adadin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar tukunyar Gas sun kai mutane 9 yayin da mutane sama da 30 suka jikkata.

Shugaban hukumar Kwamared Sale Aliyu Jili ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio da yammacin ranar Talata.

“A yanzu haka mun ziyarci wajen da lamarin ya faru kuma an ba mu rahoton cewa an zaro gawarwakin mutane 9 wadanda gini ya danne sanadiyyar fashewar tukunyar” a cewar Jili.

“Gwamanan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin a tattara rahotannin wadanda suka jikkata domin ya duba yadda za a iya tallafa musu”.

Kwamared Sale Aliyu Jili ya kuma ce, da zarar an kammala tattara bayanan waɗanda abin ya rutsa da su za a mikawa gwamnati domin ta basu tallafi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!