Connect with us

Labaran Wasanni

Fatih Karagumuk ta sallami Ahmad Musa daga kungiyar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Fatih Karagumruk dake kasar Turkiya, ta katsekwantiragen dan wasan gaba na Super Eagles Ahmad Musa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Internet a ranar Juma’a 2 ga watan Satumbar shekarar 2022.

Ahmad Musa dai shekara 1 ce ta rage masa da kungiyar.

Mai shekaru 29 ya koma kungiyar ta Fatih Karagumruk a kakar wasan data gabata a matsayin kyauta.

Idan za’a iya tuawa dai kungiyar Al-Nassr dake kasar Saudia ta taba katse kwantiragen dan wasan kafin karewar ta.

Dan wasan ya shafe wasu lokuta da tsohuwar kungiyar sa ta Kano Pillars kafin ya koma kasar Turkiya.

Dan wasan ya wakilci kungiyar wasanni uku a kakar wasa ta bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!