Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

A A Chiko Cup – Freedom Radiyo ta lallasa rukunin gidajen Radiyon Arewa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Freedom Radio da Dala FM sun lallasa rukunin gidajen Radiyo na Arewa Radiyo da suka haɗar da Wazobia FM da kuma Cool FM a wasan sada zumunci na bikin daya daga cikin masu gabatar da shirin labarin Wasanni na tashar Arewa Radiyo mai suna A A Chiko.

Tun da fari rukunin gidajen Radiyon na Arewa ne ya fara shiga gaban Freedom Radio da ci biyu babu ko daya kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Inda bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ne tawagar yan wasan na Freedom Radiyo da suka haɗar dana tashar Dala FM suka warware kwallayen 2.

Bayan shafe mintuna 90 ana fafata wasan ne aka je bugun daga kai sai me tsaron raga inda Freedom Radiyo da tashar ta Dala FM suka samu nasara da ci 2-1.

Da wannan nasara ne Freedom Radiyo da tashar ta Dala FM suka lashe kofin da aka sanya domin taya murnar Auren daya daga cikin masu gabatar da labarin Wasanni a tashar ta Arewa Radiyo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!