Labaran Wasanni
FIBA WORLD CUP: D Tigers ta doke ƙasar Uganda

Ƙungiyar ƙwallon kwando ta Najeriya, D Tigers ta samu galaba akan tawagar ƙasar Uganda, a wasannin neman cancantar shiga kofin Duniya na FIBA World cup.
Najeriya ta samu galaba da maki 95 da 69, a wasan ta na Uku, a ƙoƙarin samun tikitin zuwa kofin duniya.
Nasarar na zuwa bayan wacce D Tigers din ta samu akan ƙasar Mali da maki 72 da 70, inda dan wasa Ike Diogu, ya samo maki 19 a wasan.
Tun a farkon wasannin tawagar ta D Tigers, ta fara da rashin nasara inda ta sha kashi a hannun tawagar ƙasar Cape Verde.
You must be logged in to post a comment Login