Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FIFA Ranking: Super Eagles ta dawo mataki na 32

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta dawo mataki na 32 a duniya a cikin jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar a ranar Laraba.

A baya dai Najeriya ta na a mataki na 3 a Afrika amma yanzu ta dawo ta 4, yayin da kasar Algeria ta dare matakin na 3.

Haka kuma a cikin jadawalin da FIFA ta wallafa a shafinta na Internet a watan Satumba bayan kwashe watanni 6 a na hutun Coronavirus, Najeriya ta samu damar matsawa zuwa mataki na 29 a duniyar kwallon kafa.

Najeriya ta buga wasannin sada zumunta da kasar Algeria da Tunisia, inda ta yi rashin nasara kan Algeria da ci 1 da nema sai kuma ta yi canjaras da Tunisia da ci 1-1.

Hakan ne ya sanya Najeriya ta dawo kasa daga mataki na 29 zuwa mataki na 32 a cikin jadawalin da FIFA ta wallafa ranar Labarar da ta gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!