Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FIFA ta fara gina filin wasa a jihar Kebbi

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi ta jagoranci tawagar hukumar kwallon kafa ta kasa wajen kaddamar da fara ginin matsakacin filin wasan da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dauki nauyin ginawa tare da goyon bayan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF.

Gwamnan jihar ta Kebbi Abubakar Atiku Bagudu tare da mukarraban sa ne suka jagoranci wakilan tawagar shugaban hukumar NFF zuwa wajen da za’a gudanar da aikin a Birnin Kebbi.

Atiku Bagudu ya jinjina wa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma NFF bisa amincewa a gudanar da aikin gina filin wasan a jihar.

Haka kuma shugaban hukumar NFF Amaju Pinnick da Ibrahim Musa Gusau ya wakilta, ya ce, ya na taya daukacin mutanen jihar murnar samun tagomashin irin wannan aiki daga FIFA.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!