Labarai
FIFA ta tsawaita wa’adin dakatarwar da ta yiwa Blatter da Valcke
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta kara shekaru 6 akan wa’adin dakatarwa da ta yiwa tsohon shugabanta Sepp Blatter da tsoho Babban Sakatare Jerome Valcke.
FIFA dai ta dakatar da Sepp Blatter da Jerome Valcke ne sakamakon zargin badakalar kudade masu yawa a hukumar.
A wata sanarwa da kwamitin Da’a na hukumar ya fitar na cewa, Blatter mai shekaru 85 ya karbi cin hancin kudaden sama da dala miliyan 24 a wasannin gasar shekarar 2010 da 2014.
Sanarwar ta kuma ce, Valcke mai shekaru 60 da ya kasance na hannun damar Blatter, ya karbi cin hancin makudan kudade a matsayinsa na Babban sakatare.
Haka kuma, kwamitin Da’ar ya ce Blatter da Valcke sun sabawa doka da ka’idojin hukumar ta FIFA bisa samunsu da aikata wadannan laifukan.
“Wannan sabon karin wa’adin dakatarwar zai fara aiki ne yayin da tsohon wa’adin dakatarwar ta baya ya kare,” a cewar kwamitin.
You must be logged in to post a comment Login