Labarai
Kwankwaso ya ƙaddamar da ƙungiyar TNM
Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiyar siyasa gabanin zaɓen 2023.
Kwankwaso wanda yanzu haka yeke jagorantar wani gagrumin taro na wasu manyan siyasar Najeriya ƙarƙashin wani yunƙuri mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da kyaftin Idris Wadatsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
A jawabin Kwankwaso ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar suka haɗa kai don ceto ƙasar daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da ƙasashen waje.
A cewar Kwankwaso za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara
Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya kamar yadda BBC ta rawaito.
You must be logged in to post a comment Login