Labarai
Gamayyar Jami’yyun siyasa na zargin hukumar INEC da amfani da matasan N-Power don aikin wucin gadi
Gamayyar jam’iyyun siyasa sun yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na shirin amfani da wandanda suka cin gajiyar shirin bai wa matasa aikin yi na N-POWER a matsayin ma’aikatan wucin gadi a babban zaben da za’a yi a wata mai kamawa
Wannan bayanin na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawon gamayyar jam’iyyun Ikenga Ugochinyere ya fitar cewa tuni hukumar zabe ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin na N-POWER, yayin da ya ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dai-daitawa hukumar INEC zama.
Mr, Ikenga Ugochinyere ya kara da cewar, kamar yadda shugaban hukumar zabe farfesa Mahammod Yakubu yayi wa ‘yan Najeriya alkawarin gudanar da sahihin zabe kuma karbabe, amma daukar ma’aikatan N-power a matsayin na wucin gadi a fayyace yake za su yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari aiki da jam’iyyar APC yayin zaben dake tafe.