Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar INEC ta karyata zargin jam’iyyun siyasa na shrine daukar ma’aikatan N-Power

Published

on

A wani labarin kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta karyata zargin da ganayyar jam’iyyun siyasa suka yi mata na  cewa tana shirin daukar ma’aikatan N-POWER a matsayin ma’aikatan wucin gadi.

Daraktan katin zabe da wayar da kan jama’a na hukumar ta INEC Mr, Oluwole Osaze-uzi bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar cewa hukumar zabe  na daukar masu bautar kasa ma’aikatan wucin gadi don gudanar da zabe.

Mr, Oluwole Osaze-Uzi ya kara da cewar, sai dai in sami gibi ne, zai sanya ta yi amfani da daliban manyan makarantu, ko kuma tsofafin masu bautar kasa, amma babu wani shiri na amfani da ma’aikatan da suka ci gajiyar shirin na N-POWER.

Kuma kowa yasan cewar, tun bayan da aka  kafa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na amfani da masu bautar kasa wajen gudanar da zabe a matsayin ma’aikatan wucin gadi, kuma bayar da za’a yi kwatsam wannan gwamnati ta sauya wancen tsari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,813 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!