Kiwon Lafiya
Gamayyar kungiyar kwadagon jihar Ondo ta yi barazanar tsunduma yajin aiki
Gamayyar kungiyar kwadago ta jihar Ondo sun yi barazanar tsunduma yajin aikin daga gobe Talata in har gwamnatin jihar ta gazza biyan ma’aikata albashi.
Kungiyar kwadagon ta nemi gwamnan jihar Rotimi Akeredoli da ya iya ma’aikatan jihar Albashin su daga cikin kudin Paris Club da ta karba daga hannun gwamnatin tarayyan a kwanna baya.
Wannan na kunshe cikin wasikar da suka aikewa gwamnann mai dauke da kwanan wata na ranr 9 ga wannan watan, kuma mai dauke da sa hannun hadin gwaiwa na shugabanin gamayyar kungiyar kwadagon na jihar Tayo Ogunleye da Soladoye Ekundayo
Ma’aikatar jihar dai na zargin gwamnan jihar Rotimi Akeredoli da rashin tuntubar gamayyar kungiyar kwadagon a lokacin da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar tun da fari kamar yadda aka cimma.
A cewar ma’aikatan jihar ba za’a zauna lafiya ba in har gwamnati ta gazza biyan albashin su daga gobe Talata wajen sake tsunduma yajin aiki kamar na watan Yunin shekara ta 2016.