Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje : Abubuwa 8 da ba’a sani ba kan kudirin kasafin kudi na Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa zata kashe fiye da Naira 147,935,302,948 a kudirn kasafin kudin badi 2021, wanda aka yi wa take da” farfado da tattalin arziki da kuma dorewar cigaban rayuwar al’umma” 

Ganduje ya gabatar da kudirin kasafin kudin badin ne a kwaryar majalisar dokoki ta Kano a yau Talata.

Ganduje ya ce kasafin kudin badin zai maida hankali wajen baza komar tattalin arziki wajen samar da kudaden shiga da zummar kafa harsashin cimma manufofin gwamnati mai ci.

Abubuwa 8  kan kudirin kasafin kudin Kano 

  1. Manyan ayyuka ya samu kason Naira biliyan 74.6
  2. Ayyukan yau da kullum na da kaso biliyan 73.2
  3. Bangaren Ilimi zai sai samu kason Naira biliyan 37 kasancewar  zai kwashe kaso 25 cikin 100 na kasafin.
  4. Bangaren lafiya na da kaso biliyan 25.5 kasancewar ya kwashe kashi 17 na kudirin kasafin kudin bana.
  5. Bangaren Ilimi ya samu kaso n Naira biliyan 37  wanda ya samu kashi  25 na kudirin kasafin kudin 2021.
  6. Bangaren ayyukan Noma zai lashe Naira biliyan 5.7
  7. Ma’aikatar gidaje da Sufuri zai ta kashe Naira biliyan 3
  8. An kebewa Ma’aikatar yada labarai Naira biliyan 2.5

Kudirin kasafin kudin zai maida hankali akan wasu muhimman batutuwa

Kudirin kasafin kudin zai mai da hankali wajen ingata sake yin nazari kan karatun tsangaya ko na Almajirai, da samar da tsaro da wadata jihar nan da abinci.

Kazalika wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai ga gwamnan Kano ya sanya wa hannu cewa,Gwamnan jihar Kano Abdullahi ya ce Jihar Kano na yaki da cin hanci da rashawa, duba da cewar gwamnati mai ci ta kafa hukuma mai zaman kanta da zata yi yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Kudirin kasafin kudin ya tanadi shirye-shiryen kiwon lafiya da bada horon dogaro da kai.

Sauran su ne, hada hannu da bangarori masu zaman kan su da aiwatar da manufofin dorewar cigaban jihar Kano baki daya.

Kai Tsaye : Ganduje zai kashe fiye da Naira biliyan 147 a kasafin kudin badi

Shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattawa bukatar kara biliyan 164 cikin kasafin bana

Majalisar dattijai zata mikawa shugaba Buhari kunshin kasafin bana a Juma’ar nan

El-rufa’i ya gabatarwa majalisa kasafin kuɗin shekara mai zuwa

Jawabin Shugaban majalisar dokoki ta Kano kan kudirin kasafin kudin 

Da yake jawabi shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Abdulaziz Garba Gafasa ya ce majalisar zata fara yin nazari kan kudirin kasafin kudin badin wajen  yin Taza da Tsifa.

Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce nan bada jimawa ba majalisar zata kira shugabanin ma’aikatu da hukumomi da sashi-sashi wajen kare kasafin a gaban kwamitocin majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!