Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye : Ganduje na gabatar da daftarin kasafin kudin 2020

Published

on

A halin da ake cikin gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya sauya harshe zuwa harshen hausa yana mai cewa ya zama wajibi ya bayyana yadda kushin daftarin kasafin kudin cikin harshen Hausa.

Ka zalika  Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje na gabatar da kunshin kasafin kudin badi wanda ya kai naira biliyan dari da casain da bakwai da miliyan Dari shida da tamanin da Uku da dubu Dari Uku da hamsin da Uku da Dari shida da hamsin da Tara.

A cewar gwamnan za a yi amfani da kudaden wajen gudanar ayyukan raya kasa a fadin jihar Kano a shekara mai zuwa.

Gwamna Ganduje ya ce bangaren manyan ayyuka zai samu jimillan naira biliyan Dari da goma sha bakwai da miliyan Dari bakwai da goma da dubu Dari shida da ashirin da shida da Dari takwas da tamanin da daya.

A cewar gwamnan na Kano ayyukan yau da kullum za su samu naira biliyan sabain da Tara da miliyan Dari Tara da sabain da biyu da dubu Dari bakwai da ashirin da shida da Dari bakwai da sabain da takwas.
Ya ce kasafin kudin mai taken: Dorewar bunkasar ci gaban alumma zai tai maka gaya wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Gwamnan na Kano ya kuma ce maaikatar lafiya za a kashe sama da kaso goma sha biyar na kasafin kudin wajen kyautata kiwon lafiyar alummar jihar.

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano ya ruwaito cewa harkar samar da ruwan sha zai lakume sama da naira biliyan goma sha biyar.

Gwamnan Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya fara jawabin kan irin cibagan da ya aka samu a shekarar da ta gabata cikin kunshin kasafin kudin wannan shekarar.

Yana mai cewa gwamnatin sa ta sami nasarar aiwatar da manyan ayyuka daga cikin kasafin kudin da aka gebewa wannan shekarar.

Ya ce cikin idan aka yi nazari cikin kasafin kudin na wannan shekara kan harkokin kasuwanci da ma’adinai an sami cigaba mai ma’an

Kazalika Gwamnan Ganduje ya kara da cewar an daga linkafar wasu asibitocin don inganta kiwon lafiya a jihar nan.

wamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya isa majalisar dokoki don gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin badi.

Gwamnan Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya isa harabar majalisar dokoki da misalin karfe goma da kwata.

Ganduje dai ya fara jawabi da harshen Turanci.

Abunda ya kamata ku sani kan kasafin kudin badi

Majalisa:An samu hargitsi yayi gabatar da kunshen kasafin kudin bad

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!