Labarai
Ganduje : An dakatar da bukukuwan sallah babba a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bukukuwan sallah da za a gudanar a lokutan babbar sallah da ke gabatowa a kwanakin nan a wani mataki na dakile yaduwar cutar Corona a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Kano Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a safiyar yau.
Muhammad Garba ya ce, za a gudanar da sallar Idi babba cikin bin ka’idojin da masana kiwon lafiya ke bayarwa na takaita yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Ya kuma ce dukkanin sakarakunan masarautun jihar guda hudu za su da suka hadar da Gaya, Karaye, Bichi da Rano za su gudanar da sallar Idi a garuruwan su.
You must be logged in to post a comment Login