Labarai
Ganduje da wasu jiga-jigan APC za su koma PDP- Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa nan da zuwa watanni shida jam’iyyar APC za ta rabu zuwa gida biyu.
Haka kuma ya kara da cewa, shugaban jam’iyyar ta APC na kasa Dakta Abdullahi Ganduje, da sauran wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar za su koma jam’iyyar PDP.
Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne lokacin da ya ke gabatar da jawabi a babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a dandalin Aminu Kano Triangle da ke birnin Dutse na jihar Jigawa.
Alhaji Sule Lamido ya kuma bukaci ‘ya’yan jam’iyyarsa ta PDP da kada su karaya saboda sauya sheka da wasu zababbun shugabanni ke yi bayan samun nasarar cin zabe karkashin jam’iyyar PDP zuwa APC.
You must be logged in to post a comment Login