Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Ba za mu aminta PDP ta kai takara yankin kudu saboda son zuciya ba – Sule Lamiɗo

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma guda daga cikin jagororin jam’iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya ce, ba za su amince jam’iyyar ta miƙa takarar shugabancin ƙasar nan a shekarar 2023 ba matuƙar aka sanya son zuciya.

Sule Lamido wanda tsohon gwamanan jihar Jigawa ne daga shekarar 2007 zuwa 2015 ya bayyana hakan a wata hira da sasahin Hausa na BBC.

“Kowa yasan cewa jami’iyyar PDP ta ‘yan Najeriya ce kuma kowa yana da ƴanci a bashi dama akan abin da bai saba doka ba, ammma ba zai yiwu muna kalllo a bai wa yankin kudancin kasar nan takara ba, muddin aka ce za’a sanya son rai ko son zuciya” a cewar Lamiɗo.

“Idan an yi duba cewa jami’iyyar tsahon shekaru 6 a baya ba ta da wani karkashi a yankin Arewacin ƙasar nan, wanda hakan ya sa akai tuni cewa a bai wa wani daga yankin damar shugabantar jami’iyyar domin dawo da karkashinta kuma wannan tsari yayi,  amma batun  lallai sai ɗan takara ya fito daga wani yankin idan aka sanya son rai ina ganin ba zai hiwuba,” in ji Sule Lamido.

Lamiɗo ya ƙara da cewa, “Irin wannan lamarin ya taɓa faruwa a baya da aka ce Olesegun Obasanjo ba zai yi takara ba amma kuma daga baya ya samu damar yin takarar saboda samun masalaha wanda hakan ba sabon al’amari ba ne.

“Magana ta gaskiya babu maganar dole a siyasa, idan su gwamnonin kudancin Najeriya suka ce lallai abin da suke so za ayi to muma ‘yan Arewacin ƙasar za mu iya haɗe kan mu mu ce lallai sai abin da mukeso, kaga  kenan idan akai haka su waye a tsakiyar kenan? hakan zai nuna cewa babu Najeriya kenan”.

Ya kuma ce idan ya kasance fitar da dan tarar daga wani yanki shine zai zama mafita to ba laifi, domin kuwa zaman lafiya da son ci gaban ƙasar mu shi ne fatanmu.

Ya kuma ce abin da ya kamata a sanya gaba shi ne son ƙasa da kuma ci gabanta, ba wai batun fifita wani yanki ba da hakan zai iya kawo naƙasu a ci gaban ƙasar mu.

Sule Lamiɗo yayi fatan cewa, duk wanda ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 to a bashi, ko da daga wanne bangare ne ba tare da an nuna son zuciya ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!