Labarai
Ganduje ya aike da sakon ta’aziyar rasuwar sarkin Zazzau

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya aike da ta’aziyar sa ga al’umma da kuma jihar Kaduna kan rashin da aka yi na Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a jiya.
Wannan na cikin sanarwar da da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar, inda Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi musamman a bangaren sarautar gargajiya.
Ganduje ta cikin sanarwar ya bayyana marigayi Alhaji Shehu Idris a matsayin jajirtaccen mutum da yayi shugabanci abin misali.
Abdullahi Umar Ganduje a madadin al’ummar jihar Kano, ya yi addu’ar samun rahma ga sarkin na Zazzau da ya rasu yana da shekaru 84.
You must be logged in to post a comment Login