Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya aike da sakon ta’aziyyar rashin yar gwagwarmaya Shema’u

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya mika sakon ta’aziyarsa game da rasuwar daya daga cikin jajirtattun masu rajin kare ‘yancin masu fama da lalurar amosasnin jini, Shema’u Adam Imam, wanda ta rasu a yau, Asabar.

Kafin rasuwarta dai Malama shema’u Adam Imam daliba ce ‘yar aji hudu a jamiar Bayero da ke nan Kano, kuma mamba a kungiyar amintattu ta masu fama da lalurar amosanin jini.

Gwamnan Ganduje ya ce rasuwar Shema’u Adam Imam babban rashi ne bawai kawai ga m,asu fama da lalurar amosanin jini ba har ma ga al’ummar  jihar Kano baki daya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Abba Anwar, ta ruwaito gwamnan na Kano na mikawa da sakon ta’ziytarsa ga iyaye da ‘yan uwar marigayiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!