Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nawoj – Za mu hada kai da kungiyoyin kare hakkin Dan Adam don magance matsalar fyade  a Kano

Published

on

Kungiyar ‘yan jarida Mata ta kasa NAWOJ ta ce za ta hada Kai da kungiyoyin Kare hakkin Bil Adama da gwamnatin Jihar Kano don samar da hanyoyin magance yawaitar fyade ga ‘ya’ya mata.

Shugabar kungiyar reshen Kano Hajiya Bilkisu Ado Zango ce ta bayyana hakan a wani taro da kungiyar ta shiryawa mata yan jaridu a yau.

A cewar ta, fyade na daga cikin mummunar rayuwa da mata musmamam yara ke  fuskanta, tana mai cewa lokaci ya yi da za a hada karfi da karfe don yakar masu aikata fyade.

Wasu mata yan jarida da suka hallarci taron bayyana gudunmowarsu akan taron dakile yawaitar samun rahotannin fyade a jihar Kano

Wakiliyar mu Aisha Muhammad ‘Yan Leman wadda ita ce shugabar yan jaridu mata a Freedom Rediyo ta rawaito cewa, mata ‘yan jaridu da dama ne suka hallarci taron inda aka tattauna kan samar da hanyoyin dakile ayyukan masu fyade.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!