Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Ganduje ya bai wa Malamai 81 mukullan gidajen da suka mallaka

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya mika mukullan Gidaje ga Malaman makaranta casa’in da daya da ya yafewa kaso casa’in cikin dari na kudaden da zasu biya don mallakar gidajen bisa tsarin cire kudi daga albashinsu.

Da yake kaddamar da rabon Gidajen a karamar hukumar Ungoggo jiya Asabar Gwamna Ganduje ‘yace malaman makaranta na da matukar muhimmanci ga ci gaban kowacce al’umma, don hakan akwai bukatar Inganta rayuwarsu da ta iyalansu’.

Malama Maimuna Sani Gadanya, guda ce cikin malaman makarantar da suka amfana da gidajen ta bayyana godiyarta bisa wannan tagomashi da gwamnan ya musu, Wacce ta ce ‘baza su taba mantawa dashi ba iya tsayin rayuwarsu’.

Freedom Radio ta rawaito cewa ‘mataimakin shugaban kungiyar kwadago na Kasa Kwamared Kabiru Ado Munjibir, Wanda aka sawa rukunin Gidajen Malaman sunan sa ya hore su kan su jajirce wajen gudanar da aikinsu.

Rahoton: Abba Isa Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!