Labarai
Ganduje ya ce kofar sulhu a buɗe take tsakaninsa da Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce a a shirye yake ya shirya da abokin siyasarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da BBC.
Ya ce, yana fatan nan gaba za su daidaita da Kwankwaso, a harkar siyasa.
Ganduje da Kwankwaso dai sun jima ba sa ga maciji da juna a harkokin siyasar jihar Kano, kuma ana ganin komawar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa jam’iyyar APC zai sake ruruta adawar da ke tsakanin su
Ganduje ya ce abin da yanzu ya fi muhimmanci shi ne ci gaban al’ummar Kano da kuma nasarar jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa, “Idan Abba ya samu nasara, mun samu; in mun samu nasara, ya samu; idan ya faɗi, mun fadi; idan mun fadi, ya fadi. Duk wanda ya gane wannan, magana ce ta mu taimaka wannan gwamnati tayi nasara.”
Ganduje ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban jam’iyyar APC na tsawon shekara biyu ya ba shi damar fahimtar tsarin jam’iyya da yadda ake tafiyar da al’amuranta.
“A kan batun ko za a ba Abba dama ya tsaya takara a jam’iyyar, na san abun da yaka a tsarin mulki da kuma abin da yake na al’ada na jam’iyyar. Al’ada ta jam’iyyar APC shine wanda yake gwamna, shi za a fara ba shi tayi idan yana sha’awa ya tsaya takara domin ya maimaita ko yayi tazarce, amma ba yana nufin duk sauran muƙame haka bane,” Ganduje ya ƙara da cewa.
Ganduje ya jaddada cewa hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa zai taimaka wajen samun nasara a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login