Labarai
Ganduje ya fara gyaran makarantun firamare a Kano
Daga Safara’u Tijjani Adam
Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai kwa ya ce tuni aka fara gudanar da gyaran makarantu a karamar hukumar kamar yadda gwamnatin jihar kano ta warewa kowacce karamar hukuma kimanin naira Miliyan Ashirin domin gyaran makarantun su da suka lalace da kuma gina sabbin Ajujuwa.
Alhaji Ado Tambai kwa ya bayyana hakan a yayin zagayen bazata da ya kai wasu makarantun da aka ake tsaka da gyarawa unguwannin Fagen kawo da ‘yan shado sai kuma Tattarawa.
Ya ce, ba wai iya harkar ilimi kadai za a yiwa gyara ba har da sauran bangarorin da za su bunkasa harkokin ilimi a karamar hukumar ta Dawakin tofa.
Ya kara da cewa, a yanzu haka ana samar da masallatan juma’a a karamar hukumar da za a kashe fiye da miliyan sittin don samarwa al’ummar karamar hukumar saukin gudanar da ibada.
Wakiliyarmu Safara’u Tijjani Adam da ta halarci zagayen ta ruwaito cewa ta gano yadda aka fara gudanar da gyaran makarantun tare da samar da wasu sabbin ajujuwa a karamar hukumar har ma da ofis din zaman malamai.
You must be logged in to post a comment Login