Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Bindiga: Sun hallaka wani jami’in ‘yan sanda

Published

on

‘Yan Bindiga sun hallaka wani dan Sanda mai mukamin Insfekta tare da raunata wasu guda uku a jihar Niger.

Rahotanni sun tabbatar dacewar, ‘yan Bindigar sunyi kwanton Bauna ne a kan Bishiyoyi tare da bude wuta ga jami’an ‘yan sandan dake Sintiri don kare al’umma akan hanyar Minna zuwa Suleja, a Jiya Laraba 24 ga watan Fabrairu dai-dai mararrabar Kaffinkoro.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan ta kasa, Frank Mba, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya bayyana sunan Insfektan da ya mutu Mohammed Mohammed.

Rundunar ta kuma sanar da kai sauran jami’an nata zuwa Asibitin IBB Specialist hospital, dake Birnin na Minna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!