Connect with us

Labarai

Ganduje ya gargadi fursunoni su guji aikata laifuka

Published

on

Shugaban gidan gyaran hali na Goron dutse Magaji Ahmad Abdullahi ya bukaci masu laifin da  gwamnan Kano ya yi wa afuwa su kasance al’umma nagari tare da gujewa abinda zai sake dawo dasu gidan a matsayin masu laifi.

Magaji Ahmad Abdullahi ya bayyana hakan ne a yau ya yin da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ke afuwa mutane 29 da suka cancanci a biya musu tara.

Ya kuma Kara da cewa dama mutane 43 ne za’a biya wa tarar inda 14 daga cikin su yan’uwansu suka biya musu Sai kuma 29 da Gwamnan ya  yi wa afuwa.

Da yake jawabi gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce in akayi laakari da Zama na gari da wasun su ke yi yayin barin su gidan gyaran halin hakan na nuna cewa ana samun nasara

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Gwamnan ya kuma bukaci su da su kasance alummar da zaa rika alfahari dasu yayin barin su gidan gyaran hali.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,753 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!