Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Al’umma su dage wajen taimakawa mabukata – Limami

Published

on

A hudabar sa ta idin babbar   sallah  Limamin Masallacin idi na sabuwar Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Auwal Abubakar ya yi kira ga al’ummar musulmi dasu dage wajen taimakon al’umma tare da kabbara ga Allah domin samun kusanci ga Allah ubangiji.

Farfesa Auwal Abubakar ya bayyana haka ne jimkadan bayan idar da sallar idin babbar sallah.

Limamin ya kuma ce wajine al’ummar musulmi su kasance sun bi Allah sannan zasu samu nasara a dukkan lamauransu na rayuwa.

A nasa jawabin shugaban majalisar malamai ta jihar Malam Ibrahim Khalil Kira yayi ga al’umma dasu zama masu bin ka’idar da Jami’an lafiya suka shinfida na kariya daga annobar Covid 19.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa an gabatar da sallar da misalin karfe 8:30 na safe tare da bin dokar sanya safar hanci da baki

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!