Labarai
Malaman Boko zasu fara koyarwa a makarantun Tsangaya-Kano
Gwamnatin jihar Kano zata dauki malamai dari shida da za su koyar a makarantun Almajirai da za’a sauya wa fasalin karatu a wani mataki na kokarin hana Almajirai yin gararranba akan Titunan jihar nan suna mabara.
Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da malaman dari shida a fadar gwamnatin jihar Kano.
A cewar gwamnan na Kano an dauki malaman ne karkashin shirin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.
Gwamnan wanda ya sami wakilcin shugaban ma’aikata na jiha Dr, Kabiru Shehu y ace gwamnati ta damu matuka ga makomar Almajirai da suke Bara akan titinan jihar nan, yayin da suke fakewa ko amfani da zuwa makarantun Al-qur’ani.
Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400
Gwamnatin Kano zata samar da Sabuwar shelkwatar hukumar Hisbah ta bayar da horo na musaman
Ya ce an zabi makarantun Almajirai dari uku da casa’in da uku daga kananan hukumomi Arba’in da hudu na jihar nan don fara shirin.
Da yake bayani wakilin gwamna y ace za’a koyar da daliban darusan Ingilishi da Lissafi da wasu muhimman darusa a ranakun Alhamis da Juma’a.
Har ila yau, ya kara da cewar malaman dari shida da aka dauka bas a cikin malamai dubu uku da gwamnati ta dauka a kwanakin baya.