Labarai
Hukuncin Kisa ne ga masu Satar mutane-Ganduje
Gwamnatin Kano ta baiwa kowanne guda daga cikin yaran da aka ceto su bayan da aka sace su a kai su jihar Anambara a baya-bayan nan su tara Naira miliyan guda.
Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a jiya yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum goma sha shida 16 da za su gudanar da bincike kan yadda aka sace yara fiye da Arba’in 40 aka saida su a can jihar Anambra tun daga shekara ta 2010 zuwa ta 2019 da muke ciki.
Da yake jawabi bayan kaddamar da gwamnatin, gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa kwmaitin kwanaki Talatin da ya kamala binciken sa ya mikawa gwamnati rahoto karkashin jagorancin mai shari’a Wada Umar Rano mai ritaya.
Yaushe Ganduje zai nada Kwamishinoni?
Yaran Kano 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike na musamman
Ganduje ya hana iyayen yara Magana da yan jarida
Haka zalika gwamnan na Kano ya yi alkwarin daukar nauyin yaran Tara da su yi karatu tun daga makarantar Firamare zuwa matakin Jami’a, ya kuma sake nanata cewar gwamnatin sa zata sake yi wa dokar sake mutane d ayin garkuwa da su garanbawul don zartar da hukuncin kisa ga wanda ya sace mutane.nan bada jimawa ba.
Wakilin mu na fadar gwamnati Aminu Halilu Tudunwada,ya rawaito cewar an rantsar da kwamitin mutum goma sha sheda 16 da suka hada da rundunar sojan kasar nan da ta shige da fice da jagororin alummar kabilar Igbo da malaman addinai da kungiyoyin kishin alumma da masu rike masarautun gargajiya da kuma manyan jami’an gwamnati.