Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Daura yace Oshinbajo na da biyayya

Published

on

Mai martaba sarkin Daura yace Oshinbajo na da biyayya

Mai martaba sarkin Daura Alhaji Faruq Umar ya yabawa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo saboda biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa.

Rahotannin sun bayyana cewar mataimakin shugabn kasa Farfesa Yemi Oinbajo ya je garin Daura ne don bikin nadin Musa Haro wanda da  ne a gun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An dai nada Alhaji Musa Haro a matsayin Danmadamin Daura wanda tana cikin saurata mafi girma a cikin masarautar Daura.

Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar ya sake bayyana Osinbajo a matsayin amintace mai rikon gaskiya da Amana  wanda yake da kishin Najeriya a cikin zuciyar sa.

Sarkin na Daura yace masarautar Daura zata cigaba da marawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen cimma manufofin da ta sanya a gaba.

Ina yabawa ‘yan sandan jihar Kano –Magajin garin Daura

Rundunar yan sandan Kano ta kubutar da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar

Masarautar Daura ta bayyana cewar an nada Alhaji Musa Haro a matsayin Danmadamin Daura ne saboda gudunmawar da yake bai masarautar Daura da ma jihar Katsina baki daya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!