Labarai
Ganduje ya kawo karshen barazanar yajin aikin malaman KUST
Majalisar zartaswa ta Kano ta amince da ware kudi da yawan su ya zarta naira miliyan 245 don fara biyan malaman jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil da wadanda ba malamai ba hakkokin su na tsahon zangon karatu uku.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya ce ba’a biya ma’aikata da malaman jami’ar hakkokin su ba, a bara kamar yadda yake cikin yarjejeniyar da kungiyar ASUU ta kulla da Gwamnatin tarayya.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 30 ga watan Janairun da ya gabata ne jami’ar ta Wudil ta yi barazanar tafiya yajin aiki, matukar aka gaza magance matsalar karancin kudi da ta ke fama da shi da kuma rashin biyan ma’aikata alawus-alawus din su.
Haka kuma Majalisar zartasawa ta kuma ware sama da naira miliyan 552 don gyaran madatsar ruwa ta Kafin Chiri da ke karamar hukumar Garko.
Kana Majalisar ta amince ta ware sama da naira miliyan 122 don gyara da kawata sabon ginin da aka kammala a sashen kotuna da ke cikin sakatariyyar Audu Bako.
Haka kuma Majalisar ta kara amincewa a ware sama da naira miliyan 121 don gyara guraren da ke fama da zaizayar kasa a karamar hukumar Garko.
Akwai kuma batun ware maira miliyan 38 don samar da baturan fitilu masu amfani da hasken rana a hukumar samar da katin dan kasa da ke nan Kano.
Sauran kudaden da aka ware a jiyan sun hadar da sama da naira miliyan 16 don fadada ayyukan koyar da matasa sana’o’i.
You must be logged in to post a comment Login