Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya maida martani kan zargin saida otel din Daula

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatinsa tana mai da kadarori mallakin gwamnatin jihar da aka yi watsi da su ne don samar da abubuwan more rayuwa wanda wani mataki ne na mai da jihar Kano daya daga cikin manyan birane na duniya.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Kano Aminu Yassar.

Sanarwar ta ce maimakon kyale kadarori da gwamnati ta kashe makudan kudade wajen samar dasu, su lalace, zai fi kyautatuwa a mai dasu wuraren amfanin al’umma.

Haka zalika sanarwar ta kuma ce hakan zai taimaka gaya wajen samarwa da gwamnati kudaden shiga baya ga samar da aikin yi ga dumbin matasan jihar.

A baya-bayan nan ne dai dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Abba Kabir Yusuf ,ya shigar da kara gaban kotu yana zargin matakin da gwamnatin jihar ta dauka na mallakawa ‘yan kasuwa wasu kadarorin gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!