Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje ya mikawa sabbin sarakunan wasikar shedar nadi

Published

on

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa sabbin Sarakunan Kano da Bichi wasikar shedar nadi a yanz- yanzu.

Da fari dai Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wasikar shedar nadi a matsayin sarki mai daraja ta daya.

Bayan mikawa sarkin na Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ne sai gwamnan ya mikawa na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Wakiliyar mu ta Fadar gwamnati Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, dakin taro ya cika makil da magoya baya da kuma hakimai.

Da  Bayan la’asar din nan ne aka fara bikin bada wasikar shedar danin ga sabbin sarakunan da gwamnatin Kano ta yi.

A dai ranar Litinin 9 ga watan nan da muke ciki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tsige tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II daga mukamin sarkin Kano bayan da ya kwashe kusan shekaru 6 akan mukamin.

Muna dauke da cikkaken labarin anan gaba kadan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!