Connect with us

Labaran Kano

Ganduje na shirin mikawa sabon sarki wasikar shedar nadi

Published

on

Ana saran nan gaba kadan  a yau Laraba Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai mikawa sabon sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma sabon sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero  wasikar nada su sabbin Sarakuna masu daraja ta daya.

Wakiliyar mu ta Fadar gwamnati Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, Bayan la’asar din nan ne ake sa ran gwamnatin Kano za ta mika musu Wasikun.

Tuni dai dakin taro na Coronation ya dauki harami don baiwa sabbin sarakunan na Kano da Bichi wasikun.

An sauyawa tsohon Sarkin Kano wuri a jihar Nasarawa

Sabon Sarkin Kano yaje gidan mahaifiyar sa don neman tabarraki

Yanzu yanzu sabon sarkin Kano ya yi zagayen rangadi

A dai ranar Litinin 9 ga watan nan da muke ciki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tsige tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II daga mukamin sarkin Kano bayan da ya kwashe kusan shekaru 6 akan mukamin.

Muna dauke da cikkaken labarin anan gaba kadan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!