Labarai
Ganduje ya musanta batun komawarsa PDP

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da batun cewa zai iya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP kafin zaben shekarar 2027.
A cewar ganduje a wannan lokaci jam’iyyar ta PDP ta riga ta gama mutuwa, a daidai lokacin da kuma jam’iyyarsa ta APC ke ci gaba da mamaye kasa.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa Edwin Olofu ya fitar yau Litinin a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar dai na zuwa ne sakamakon wasu kalamai da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya yi na cewar shugaban jam’iyyar ta APC zai koma cikin su nan bada dadewa ba.
A kalaman da tsohon gwamnan na Jigawa ya yi, ya kuma ce, nan da watanni shida masu zuwa duk wani dan jam’iyyar su ta PDP da ya koma APC zai dawo cikinta a dai-dai lokacin da PDP din za ta ci gaba da Mamaye kasa.
You must be logged in to post a comment Login