Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Siyasar Kano: Ko ina makomar siyasar Malam Salihu Takai?

Published

on

Siyasar Kano dai aka ce sai Kano, Malam Salihu Sagir Takai dai daya ne daga cikin manyan ‘yan takarar gwamnan Kank a zabukan shekara ta 2011, da 2015 da ma shekarar 2019.

A shekarar 2011 dai gwamnati mai mulki a wancan lokacin ta tsayar da Malam Salihu Sagir Takai matsayin dan takarar ta na gwamna, dukda cewar akwai rabuwar kai tsakanin manyan mukarraban gwamnatin ciki harda mataimakin gwamna da kwamishinoni a wancan lokaci.

Masu bibiyar siyasa dai na ganin wannan rabuwar kai ce, ta taimaka gaya wajen faduwar jam’iyya mai mulki ta ANPP a zabe, inda Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya lashe zabe a matsayin gwamnan Kano zagaye na biyu.

Kwankwaso ya kayar da Takai a wannan zabe, da kuri’u kusan dubu arba’in da takwas.

A kakar wannan zabe dai anyi amfani da wakoki kamar wakar “Kwankwaso dawo-dawo” da kuma wakar “Allah ka ba Takai gwamna” da sauransu, baya ga kalamai masu zafi da aka rika musayan a kakar wannan zabe.

Kalmomin da suka fi tashe kuwa sun hadar da “Wuju-wuju, goro dan ujile, mahaha, da kuma ba makami sai addu’a”

A wannan zabe dai masu bibiyar lamuran siyasar Kano na ganin cewar tasirin matasa shine babban makamin da Kwankwaso ya rika, ta yadda kamfen din sa ya mayar da hankali kacokan akan su.

Malam Salihu Takai ya tafi kotu inda ya kalubalanci wannan zabe, wanda bai samu nasara ba, a karshe kotu ta nemi ya biya tsagin gwmanati kudi, wanda gwamna Kwankwaso ya shelanta cewa a siyawa yara alawa da kudin.

Bayan wannan lokaci an samu juyin juya hali a siyasar Kano wanda yayi sanadiyyar samun sauyin sheka wadda ta kai, gwamna mai mulki Rabi’u Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP ya kuma koma jam’iyyar hadaka ta APC, a daya bangaren shi ma Malam Salihu Takai da mai gidansa tsohon gwamnan Kano Malam Shekarau, suka koma jam’iyyar adawa a Kano ta PDP.

Karin labarai:

Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Kano

Majalisar dokoki ta bukaci Ganduje ya magance matsalar ruwa a Kano

Haka aka taho har shekarar 2015 inda a wannan shekarar kuma jam’iyya mai mulki ta APC ta tsayar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje matsayin dan takarar gwamna.

Ita kuma jam’iyyar PDP ta tsayar da Malam Salihu Sagir Takai inda ya kara yin takarar gwamna a karo na biyu.

A wannan karon dai zaben a Kano za a iya cewa bai samu armashi sosai a bangaren su Malam Takai ba, kasancewar babu gwamnati a hannun su, ga kuma siyasar a mataki na kasa suna jam’iyyar PDP mai mulki wadda kuma ba ta da rinjaye a yankin Arewa a wannan lokaci.

Haka akayi zabe, Takai ya samu kuri’u sama da dubu dari biyar, yayin da Ganduje ya samu kuri’u sama da miliyan daya.

Bayan zaben 2015 sai rikicin cikin gida yayi karfi a jam’iyya mai mulki a Kano ta APC musamman tsakanin gwamna mai ci Ganduje da tsohon gwamna Kwankwaso wadda a karshe tayi sanadiyyar ficewar Kwankwaso daga APC ya koma jam’iyyar sa ta asali wato PDP.

Sakamakon hakan dai ya sanya tsohon gwamna Malam Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC, sai dai Malam Salihu Takai yayi zaman sa bisa fatan cewa zai samu takarar gwamnan sa a jam’iyyar ta PDP.

A karshe dai ta fito fili Kwankwaso ba zai bai wa Takai takarar gwamna ba, hakan ya sa shima, ya fita ya koma jam’iyyar adawa ta PRO me dan mukulli.

A nan ne Malam Salihu Takai yayi takarar gwamna a shekarar 2019.

A zabe na farko Takai ya zo a mataki na uku, wanda yake bin bayan Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu, bayan da gwmana Ganduje ya zo mataki na daya.

Sai da a yayin da aka shirya tafiya zagaye na biyu na (Inconclusive) a zaben Kano, Malam Takai ya marawa gwamnan Gabduje baya, bayan da Gandujen ya shelanta cewa zai yi gwamnati mai tafiya da kowane bangare.

Yanzu haka dai a gwamnatin Kano akwai kwamishinoni, kamar kwamishinan ruwa, da kwamishinan al’amuran addini da dukkan su ‘ya’yan jam’iyyar adawa ne ta PDP.

Shin ko ina makomar Malam Salihu Takai a 2023?.
Shin gwamnatin APC ta cika alkawarin hadaka tsakanin ta da Takai?

Su ne manyan gabobin da zamu kammala a cigaban rubutukan mu masu zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!