Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya musanta rade-radin yana sayar da kadarorin gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan cewa gwamnatin Dr, Abdullahi Umar Ganduje na sayar da kadarorin jihar.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Lawan Abdullahi Musa ya bayyana hakan a yau yayin wani rangadi tare da wasu jami’an gwamnati zuwa wasu wurare da gwamnati zata mayar tsarin hadaka da ‘Yan kasuwa.

Kwamishinan Shari’ar ya Kara da cewa gwamnatin ba sayar da kadarorin  jihar ta ke ba illa tana kokarin hadin gwiwa da ‘Yan kasuwa don cigaban jihar.

Ya ce tsarin na hadaka da ‘yankasuwar abu ne da zai taimaka wajen samawa jihar kudin shiga da sauran su.

Wakiliya Zahrau Nasir ta ruwaito cewa wuraren da aka ziyarta sun hada da Sabuwar Triumph da tsohuwar Triumph da tsohowar Daula otal da filin Shahuci da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!