Labarai
Ganduje ya naɗa sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗin Dr. Kabir Bello Dungurawa a matsayin sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano.
Hakan ya biyo bayan naɗin da aka yiwa tsohon shugaban kwalejin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa matsayin sabon shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya fitar a daren Litinin.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya amince da naɗin Hajiya Hama Ali a matsayin shugabar hukumar zuba jari ta Kano wato KANIVEST.
You must be logged in to post a comment Login