Labaran Kano
Ganduje ya nada sabbin mutum biyu a matsayin masu taimaka masa
Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya nada sababin masu taimaka masa na mussaman guda biyu kan sha’anin tafiyar da harkokin gwamnati.
Daga cikin wadanda gwamnan ya nada akwai Fai’izu Kamaluddeen Na-ma’aji a matsayin mai bashi shawara na mussaman kan al’amuran yau da kullum yayin da kuma ya nada Habibu Abubakar a matasayin babban mai taimaka masa na mussaman kan al’amuran tattalin arziki.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai na gwaman Abba Anwar ya fitar a daren jiya Asabar cewa nadin ya fara aiki ne nan take.
2023: Gadar Ganduje a APC Barau ko Gawuna?
Ganduje ya nada mata masu ba shi shawara guda 5
Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma’aikata ta Kano
Har Ila yau sanarwar ta kara da cewar Fai’izu Kamaludden N a-ma’aji wanda aka fi sani da Fai’izu Alfindiki shi ne tsohon maitaimakawa gwamnan na mussaman kan harkokin wasanni, matasa da al’adu a wa’adin gwamnan na farko kuma manba ne a cibiyar nazarin tattalin arziki na kasa da kasa da siyasa dake zaune a kasar Amurka.
Yayin nadin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su da su amfani da fasahar zamani wajen ayyukan su a matsayin wata kafa na samun cigaban da aka yi a duniya a ofisoshin su.