Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje: ya nada Sani Rogo mai bashi shawara kan siyasa

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nada Alhaji Muhammad Sani Muhammad a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin siyasa.

A ranar bakwai ga watan Afrilun da muke ciki ne dai nadin da gwamnan ya yiwa Muhammad Sani ya fara aiki.

Kamar yadda yake a takaddar shaidar nadin nasa mai dauke da kwanan watan Takwas ga watan Afrilin da muke ciki, wanda babbar sakatariya kan al’amuran da suka shafi siyasa, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota ta sanyawa hannu, ta ce, duba da irin jajircewar sa wajen aiki da gaskiya da rikon amana hakan ne ya sa aka nadashi mukamin.

Ganduje ya nada mai taimaka masa kan daukar hotuna

Majalisa ta amince Ganduje ya nada sabbin masu ba shi shawara

Takardar ta kuma ce gwamnatin Kano na fatan zai yi amfani da jajircewar da yake dashi wajen ciyar da al’amuran siyasa gaba a jihar Kano dama kasa baki daya.

Alhaji Muhammad Sani Muhammad da akafi sani da Sani Rogo Tarauni ya taba neman takarar kujerar shugabancin karamar hukumar Tarauni a majalisar wakilai ta kasa.

Kuma ya taba rike mukamin mai baiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu daga watan Oktobar shekarar 2018 zuwa watan Maris din shekarar 2019.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!