Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya nemi Abba Gida-gida ya koma APC

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nemi gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP ya koma jam’iyyarsu ta APC.

Ganduje ya mika goron gayyatar ne ga Gwamna Abba Kabir a wani taron jiga-jigan APC da ya gudanar a Kano.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce, muddun Abba Kabir ya koma APC to kuwa zai mayar da Kano mai bin tafarki jam’iyya guda.

Ganduje ya kara da cewa Apc ta kudiri aniyar hadiye dukkan kananan jamiyyun dake kasar nan.

Dakta Ganduje ya ce APC a shirye ta ke ta karbi Abba Kabir Yusuf da magoya bayansa hannu bibbiyu ba tare da wata-wata ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!