Manyan Labarai
Ganduje ya sakawa dokar kikiro masarautu hannu
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sakawa dokar kirkiro masarautu hannu.
Gwamanan ya sakaw dokar hannu a dakin taro na coronation a gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan ya sakawa dokar hannu bayan majalisar dokoki ta amince da dokar.
Da yake jawabi bayan sa hannu Gwamna Ganduje yace dokar kirkiro masarautun an yi ta ne domin kawo cigaba ga al’ummar yankunan sababbin masarautun.
A dai ranar 8 ga watan Mayu na shekarar 2019 ne tsohuwar majalisar dokokin ta jahar Kano ta amince da dokar kirkiro karin masarautu a Kano da suka hada da Karaye da Rano da Bichi da Gaya.
Amma a ranar 21 ga watan Nuwambar da ya gabata ne babbar kotun Kano ta soke kirkirar masarautun .
Dalilin da ya sa kenan gwamna Ganduje ya sake aike dokar domin amincewa da ita bisa kaida.