Kowane Gauta
Ganduje ya yi burus da aikin titin mu don bamu zabe shi ba –Sammani China
Al’ummar unguwar dan Dinshe dake yankin karamar hukumar Dala a Kano sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamna Ganduje bisa yadda aikin titinsu ya tsaya cak shakara da shekaru,
Sai dai sun yi zargin cewar rashin zabar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanya ba’a karasa aikin titin ba.
Sammani China daga jam’iyyar PDP ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio kamar yadda sashen nan na 39 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya bada damar fadin albarkacin baki.
Sammani China yace titinsu tun farko yana da kyau sosai amma wani bangaren ya lalace, sai gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni aka karce titin baki daya aka zuba musu jar kasa akai wadda a yanzu kasar take yin barazana ga lafiyar su.
Sammani yace ” idan kuma gwamnan ya gaza cigaba da aikin hanyar ta su saboda dalilin da ake wukar kugu dasu cewa basu zabe shi ba to ya bari idan gwamnatin su ta PDP ta dawo zata cigaba da yi musu aikin ” .
You must be logged in to post a comment Login