Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kowane Gauta

Ganduje ya yi burus da aikin titin mu don bamu zabe shi ba –Sammani China

Published

on

Al’ummar unguwar dan Dinshe dake yankin karamar hukumar Dala a Kano sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamna Ganduje  bisa yadda aikin titinsu ya tsaya cak shakara da shekaru,

Sai dai sun yi zargin cewar rashin zabar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanya ba’a karasa aikin titin ba.

Sammani China daga jam’iyyar PDP ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio kamar yadda sashen nan na 39 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya bada damar fadin albarkacin baki.

Sammani China yace titinsu tun farko yana da kyau sosai amma wani bangaren ya lalace, sai gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni aka karce titin baki daya aka zuba musu jar kasa akai wadda a yanzu kasar take yin barazana ga lafiyar su.

Sammani yace ” idan kuma gwamnan ya gaza cigaba da aikin hanyar ta su saboda dalilin da ake wukar kugu dasu cewa basu zabe shi ba to ya bari idan gwamnatin su ta PDP ta dawo zata cigaba da yi musu aikin ” .

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!