Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya yiwa Kwankwaso ta’aziyya

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya aike da saƙon ta’aziyya ga tsohon gwamna Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran Kano Muhammad Garba ya fitar.

Sanarwar ta ce, Gwamna Ganduje ya tafi birnin Dubai tun a ranar Alhamis, a don haka ya ke miƙa saƙon ta’aziyya ga Kwankwaso a madadin sa da iyalansa da al’ummar Kano bakiɗaya.

A cikin sanarwar, Gwamna Ganduje ya ce, wannan rashi babban rashi ne ga al’umma, kuma marigayin abin koyi ne, la’akari da kyawawan halayensa.

Gwamna Ganduje ya kuma yi addu’ar neman gafara ga marigayin.

Alhaji Musa Saleh Kwankwaso ya rasu cikin daren Alhamis yana da shekaru 93 a duniya.

Kafin rasuwarsa, shi ne hakiman Madobi, kuma ya riƙe sarautar Maji daɗin Kano, kuma shi ne Makaman Ƙaraye wanda ke cikin masu naɗa Sarki a masarautar Ƙaraye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!