Labaran Kano
Ganduje: Za mu koyar da mata sana’o’in dogaro da kai
Gwamantin jihar Kano ta ce zata bawa shirin koyar da mata sana’o’in dogaro da kai fifiko, la’akari da yadda suke bayar da gudun mowa wajen samar da cigaba da kuma gina rayuwar jama’a.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayyana hakan, lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Mata Yan jarida ta kasa karkashin jagorancin, Ife omowole, ya ce akwai bukatar a bawa mata kulawar da ta dace saboda irin gudun mowar da suke bayarwa wajen cigaban al’umma.
Tun farko a nata jawabin, sakatariyar kungiyar Ladi Bala ta sun kawo ziyarar ne fadar gwamnatin Kano a wani bangare na taron horar da Mata Yan Jarida akan kalubale da suke fuskan ta musamman ma yayin gudanar da aikin su
You must be logged in to post a comment Login