Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai ciyo bashin sama da biliyan 18

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Kano ta amincewa gwamna Ganduje ya ciyo bashin sama da Naira biliyan 18 da miliyan 700 daga bankin CBN.

Amincewar ta biyo bayan wasiƙar buƙatar ciyo bashin da gwamnan ya aikewa majallisar.

Shugaban majalisar Injiniya Hamisu lbrahim Chidari ya karannta wasiƙar a zamanta na ranar Litinin.

a cikin wasikar gwamnan Ganduje ya ce, babban bankin ƙasa CBN ne ya amince da bai wa dukkannin jihohi kuɗin domin ta da ƙomaɗar da annobar COVID-19 ta janyo musu.

Wannan ya sanya Ganduje ya nemi majalisar ta sahale masa majalisar karɓar bashin don ya sanya Naira biliyan 10 cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!