Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Wa’adin mu na tafiya yajin aiki na dab da cika – JUHESU

Published

on

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiya ta ƙasa JUHESU sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta biya musu bukatun su kafin wa’adin tafiya yajin aikin su ya cika.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar JUHEHU na ƙasa Biobelemoye Josiah ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa kamata yayi gwamnati ta dauki mataki, kafin tsayar da harkokin lafiya baki ɗaya a kasar nan, wanda wa’din da suka bayar na kwanaki 15 na dab da cika.

Ta cikin sanarwar ta buƙaci ma’aikatar lafiya da ta gaggauta fitar da sakamakon yarjejeniyar da suka cimma yayin tattaunawar da suka yi kan batun walwalar su, da na albashin ma’aikata.

Sai dai tuni ma’aikatar lafiya ta ƙasa ta bakin mai magana da yawun ta Charles Akpan ya bayyana cewa har yanzu ma’aikatar da ta karbi wata takardar bukatar su ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!